Ahmad Lawal Kar Ku sake zaben mu idan kun gaji da...

Kar Ku sake zaben mu idan kun gaji da mu>>Shugaban majalisan dattijai Ahmad Lawan ya fada ma yan Najeriya

-

Advertisements
Advertisements

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya yi gargadin cewa za a iya samun rikici idan aka watsar da majalisar dattawan kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke bukata.

Maimakon haka, ya kalubalanci wadanda ba su da kwanciyar hankali da sanatoci a majalisar dattijai ta 9 a yanzu da kar su zabe su a 2023 idan ba sa son fuskokinsu.

Lawan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake gabatar da bude wani taro  ga manyan ma’aikatan majalisar dokokin kasar da kuma hukumar kula da ayyukan majalisar a Abuja.

Ya bayyana majalisar dattijai a matsayin mai bin doka da oda wanda ya tabbatar da cewa dukkan sassan kasar suna da wakilci daidai ba kamar majalisar wakilai ba inda jihohin da suka fi yawan mutane ke samar da ‘yan majalisa mafi yawa.

Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma nuna rashin amincewa da hujjar wadanda ke neman a soke Majalisar Dattawan saboda ganin cewa albashin da sanatocin ke karba na dayawa.

Advert

Ya ce kasafin kudin shekara-shekara na majalisar kasa bai gaza kashi daya cikin 100 na kasafin kudin kasar na 2021 ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you