Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Breaking News Kin Barin Barcelona Ya Hana Ni Kwazo A Bana...

Kin Barin Barcelona Ya Hana Ni Kwazo A Bana -Messi

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Lionel Messi ya ce, rashin rabuwarsa da Barcelona ya yi tasiri kan kwazonsa na taka leda a wannan kaka.

A cikin watan Agusta ne dan wasan na Argentina ya yi yunkurin amfani da wani sashi na dokar yarjejeniyarsa da Barcelona don raba gari da kungiyar a matsayin kyauta.

Sai dai Barcelona ta ki amincewa da yunkurinsa, tana mai cewa dole ne a ajiye Euro miliyan 700 kafin sakin dan wasan.

A yayin zantawarsa da gidan talabijin na La Sexta na Sifaniya, dan wasan ya ce, ya yi fama da abubuwa a farkon wannan kaka, amma a yanzu komai ya daidaita a cewarsa.

Read more at SOURCE: This post (Kin Barin Barcelona Ya Hana Ni Kwazo A Bana -Messi) firstly published at dimokuradiyya.com.ng on 2020-12-22 15:41:18

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you