Gwamnn jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa idan aka yi garkuwa da dansa ba zai biya kudin Fansa ba.
Ya bayyana hakane a hirar da ake yi dashi yanzu haka a gidan rediyon jihar.
Yace idan aka yi garkuwa da danshi Addu’a zai rika yi. Yace dan haka duk wanda aka kama yana biyan ‘yan ta’adda kudin Fansa, Za’a hukuntashi dan hakan taimakon ‘yan ta’adda ne, kamar yanda Wakilin hutudole da ya saurari hirar ya ruwaito.