Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Labarai Ko Pele ba zai iya fafatawa da Messi ba>>Marca

Ko Pele ba zai iya fafatawa da Messi ba>>Marca

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Lionel Messi yayi nasarar kafa tarihin daya fi na Pele a jiya bayan yaci kwallon guda a wasan da Barcelona ta lallasa Valladolid daci 3-0 a gasar La Liga, wadda tasa yanzu kwallayen shi na Barcelona suka kama 644 shi kuma Pele yake da kwallaye 643 a lokacin da yake bugawa Santos wasa.

Sannan kuma a ranar litinin aka baiwa Messi kyautar Pichichi karo na bakwai wanda hakan yasa yanzu ya zamo dan dan wasan daya fi lashe kyautar a tarihi. Pichichi kyauta ce wadda ake baiwa dan wasan daya fi zira kwallaye masu yawa a kowace kaka ta gasar La Liga.

Messi ya bayyana cewa yanzu komai ya daidaita kuma hana shi canja sheka da Barca tayi ne yasa baya kokari sosai a wannan kakar. Messi ya kara tabbatar da cewa shine jagoran Barcelona bayan ya taimaka kuma yaci kwallon data sa shi ya kafa babban tarihi a harkar taka leda a wasan da suka lallasa Valladolid.

Manema labarai na kasar Sifaniya, Mraca sun bayyana cewa a halin yanzu ko Pele ba zai iya karawa da Messi ba, kuma sun fadi hakan ne sakamakon karya babban tarihin Pele da Messi yayi.

Read more at SOURCE: This post (Ko Pele ba zai iya fafatawa da Messi ba>>Marca) firstly published at hutudole.com on 2020-12-23 17:05:36

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Karanta Wannan:-  Manchester City ta dare saman teburin gasar Premier League bayan data lallasa Aston Villa daci 2-0

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you

Karanta Wannan:-  An cafke jami'in tsaron jami'ar ABU Zaria da ake hada baki dashi ana sace mutane