Shahararren dan gwagwarmaya na Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo wanda ake kira Sunday Igboho ya yi magana game da kama shi da ba’a yi nasara ba a ranar Juma’a 26 ga Fabrairu
Da yake magana kan arangamar da ya yi tsakaninsa da jami’an tsaro a kusa da tashar mota ta Guru Maharaji a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a wata hira da Punch, Igboho ya fada wa Gwamnatin Tarayya da ta fara kama Shugaban Boko Haram, Ibrahim Shekau, yan bindinga da malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi kafin su zo gare shi.
Ya kara da cewa babu inda zai je ko boya domin shi mara laifi ne.