Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Kungiyar Ma’aikatan Shari’a Sun Fara Yajin Aiki Na Sai Baba-ta-gani

Published

on

Ma’aikatan shari’a sun rufe Kotun Koli da safiyar yau, Talata a Abuja, bisa la’akari da barazanar da suka yi na shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a duk fadin kasar don matsawa ‘yanci ga bangaren shari’a na gwamnati.

Wannan ci gaban ya zo ne a matsayin yin fatali da rokon da Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) ta yi masu na dakatar da yajin aikin, wanda ta ce bai kamata ba idan aka yi la’akari da takunkumin COVID-19 akan Najeriya a shekaran da ya gabata.

Ma’aikatan wasu mahimman cibiyoyin shari’a biyu – Majalisar Shari’a ta Kasa (NJC) da Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Tarayya (FJSC) – wadanda su ma suke zaune wuri daya tare da Kotun Koli suma ya shafe su.

Hakanan an ga motocin safa na ma’aikata suna kauce hanya lokacin da suka isa ƙofar shingen Kotun Koli.

Ma’aikatan na NJC da FJSC na daga cikin kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JUSUN), kungiyar hadin kai ta dukkan ma’aikatan shari’a a dukkan matakai a kasar, kuma su ma suna cikin yajin aikin da kungiyar ta bayyana.

Matakin da kungiyar ta dauka a Kotun Koli da safiyar Talata ana sa ran zai yi aiki a duk kotunan Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Kungiyar Ma’aikatan Shari’a Sun Fara Yajin Aiki Na Sai Baba-ta-gani) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-06 09:35:23

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.