Bauchi Kungiyar Matasan Kudu maso Yamma sun yi kira ga...

Kungiyar Matasan Kudu maso Yamma sun yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Moh’d da ya fito takarar shugaban kasa a babban zaben 2023

-

Wata Kungiyar Matasan Kudu maso Yamma mai rajin tabbatar da shugabanci na gari sun yi kira ga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Moh’d Abdulkadir da ya fito takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Hakan na cikin kudurorin da kungiyar ta cimma a karshen taron da kungiyar ta gudanar a karshen mako a jihar Legas.

A wata sanarwa da aka fitar a karshen taron wanda kuma shugaban kungiyar Gbenga Olawole da Sakataren sa, Tunde Olatunji suka sanya wa hannu, kungiyar ta ce zabin da suka yi wa Gwamna Bala Muhammad ya dogara ne da yadda yake da jajircewa wajan kawo sauyi tare da karfin fada aji a kasa.

Sanarwar ta kuma Kara da cewa, Sun zabi gwamnan ne kasancewar mutum ne mai gaskiya da rikon Amana wanda zai kai ga kasar tudun mun tsira idan muddin a ka zabe shi a matsayin shugaban kasar a kakar zaben 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you