Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Breaking News Labarai:-Dalilin dayasa bazamu kulle tashoshin jirgin sama ba inji...

Labarai:-Dalilin dayasa bazamu kulle tashoshin jirgin sama ba inji gwamnati.

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

– Gwamnatin Tarayya tace ba za tayi saurin hana jiragen Ingila sauka ko tashi ba

– Gwamnati ta ce yin hakan zai sa wasu su koma bin jiragen Benin, Togo ko Ghana

– Lai Mohammed ya na ganin wannan mataki zai iya taba tattalin arzikin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce ta zurawa makwabtanta idanu ne kafin ta dauki mataki game da hana jirgi tashi daga ko sauka a kasar Ingila.

Jaridar Vanguard ta rahoto Ministan yada labarai da al’adu na kasa ya na wannan bayani a jiya.

A cewar gwamnatin tarayyar, akwai bukatar samun hadin-kai tsakanin Najeriya da kuma kasashen da ta ke makwabtaka da ita a kan lamarin.

Da aka yi hira da Lai Mohammed, a shirin siyasar kasa gidan rediyon tarayya a Abuja, ya bayyana cewa ba su so su yi gaggawar daukar wani mataki.

Labarai:-Dalilin dayasa bazamu kulle tashoshin jirgin sama ba inji gwamnati.

Alhaji Lai Mohammed ya ce: “Ko da yake gwamnati ta damu da shigo da sabon nau’in COVID-19 cikin Najeriya, ba ta son yin aikin garaje.”

Lai Mohammed ya bayyana cewa kwamitin PTF ya yanke hukuncin cewa za ta sa ido, ta ga abin da ke faruwa, kafin a kai ga daukar wani mataki.

“Ba mu so mu yi saurin daukar matakin hana jirgin Ingila tashi ko sauka a Najeriya, sai kuma mu ga ana shigo mana ta Cotonou, Lome ko Accra.”

“Hakan zai kawowa ‘yan Najeriya wahala domin za ka kai dukiya zuwa wata kasa, ka yi asarar kudi.” Lai ya na tsoron fasinjojin su canza hanya.

Read more at SOURCE: This post (Labarai:-Dalilin dayasa bazamu kulle tashoshin jirgin sama ba inji gwamnati.) firstly published at www.news.arewasound.com on 2020-12-23 06:40:53

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you