Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Breaking News Labarai:- Rundunar ‘yan sanda na jihar Edo ta yi...

Labarai:- Rundunar ‘yan sanda na jihar Edo ta yi magana game da abin da ya faru jiya kan batun satar mutane.

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

– Rundunar ‘yan sanda na jihar Edo ta yi magana game da abin da ya faru jiya

– An sace wasu fasinjoji a hanyar Auchi, sannan an tare wasu fasinjojin Abuja

– Kakakin Dakarun jihar ya ce har yanzu labarin ta’adin bai kawo gare su ba

Dakarun ‘yan sanda na jihar Edo ta ce ba ta samun labarin abin da aka ce ya auku da wasu fasinjoji a kan hanyar Benin zuwa Auchi ba.

A ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020, ‘yan bindiga suka tare titin Benin zuwa garin Auchi, su ka yi gaba da wasu matafiya a motar haya.

Punch ta ce wadannan mutane da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sun kai harin ne bayan an tare wata motar da za ta je Abuja a jiyan.

Jaridar ta rahoto cewa an kai wa wadannan fasinjojin garin Abuja farmaki ne a cikin jihar Benin – tsakanin garin Ehor da kuma Iruekpen.

Labarai:- Rundunar ‘yan sanda na jihar Edo ta yi magana game da abin da ya faru jiya kan batun satar mutane.

Mai magana da yawun bakin ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya fadawa ‘yan sanda cewa ba a sanar da shi wadannan hare-hare ba.

Da ‘yan jarida su ka tuntubi jami’in a ranar Talata, sai ya ce: “Ba ni da labari. Ba a rahoto wasu daga cikin abubuwan da aka ce sun faru ba.”

“Ko da an fitar da rahoto, tun da a ofisoshin kananan hukumomi ne, ba da wuri zai kai gare mu ba.”

Nwabuzor ya ce: “Saboda haka, ku ba mu ‘dan lokaci mu yi magana da dakaru da jami’an da ke wuraren da wadannan abubuwa su ka auku.”

Wanda abin ya faru a idonsu, sun bayyana cewa an shiga da wadannan fasinjojin da aka tare cikin daji bayan an fito da su daga motarsu.

A jiya kun ji yadda wasu ‘Yan Sanda su ka kunyata Direba saboda kawai rashin bada rashawa, wanda ya jawo aka yi masa asara da tsirara.

Jami’an tsaron sun tube wannan Direban mota ne, sun yi masa barna, ba don komai sai saboda ya ki bada cuwa-cuwar da aka saba karba a titi.

‘Yan Sandan sun cire masa kaya, an yi masa zigidir haihuwar uwarsa da rana—tsaka a kan titi.

Read more at SOURCE: This post (Labarai:- Rundunar ‘yan sanda na jihar Edo ta yi magana game da abin da ya faru jiya kan batun satar mutane.) firstly published at www.news.arewasound.com on 2020-12-23 06:32:26

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you