Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

#ASUU Labarin dake shigo mana yanzu yanzu: ASUU Ta Janye...

Labarin dake shigo mana yanzu yanzu: ASUU Ta Janye Yajin Aiki

-

Labarin dake shigo mana yanzu yanzu: ASUU Ta Janye Yajin Aiki

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta janye daga yajin aikin da ta kwashe watanni tara tana yi.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai da safiyar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020 a birnin tarayya Abuja kamar yadda Legit hausa ta ruwaito.

Sanarwan ya biyo bayan ganawar kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya tun daren Talata.

Ogunyemi ya kara da cewa mambobin kungiyar ASUU sun janye yajin aikin ne da sharadin gwamnati ta cika alkawuranta.

Muddin gwamnati ta saba, a cewarsa, zasu koma yajin aiki ba tare da sanarwa ko talala ba.

Kungiyar ta malaman Jamian dai ta tsunduma yajin aikin tun watan Maris na shekarar 2020 kan abinda ta kira rashin mutunta alkawuran da gwamnatin tarayya tayi.

An dade ana kai ruwa rana kan batun yajin aikin nasu wanda sai yanzu suka janye.

Wannan labarin abun farin ciki ne ga daliban jamia wadanda suka shafe watanni a gida zaune saboda wannan yajin aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you