Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Kaftin din Barcelona, Lionel Messi ya haskaka sosai a wasan da kungiyar tashi ta lallasa Real Valladolid daci 3-0, yayin da ya taimakawa Clement Lenglet ya fara ciwa Barca kwallo a wasan kafin Braithwaite ya kara cin tashi kwallon tun kafin aje hutun rabin lokaci.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Messi yayi nasarar cin kwallon shi ta 644 a Barcelona, wanda hakan yasa karya tarihin zakaran dan wasan Brazil Pele wanda shi ya ciwa kungiyar Santos kwallaye 643 a lokacin da yake buga mata wasa.
A karshe dai an tashi wasan ne Barcelona tana cin uku wanda hakan yasa tayi nasarar ta biyar a teburin gasar yayin da Atletico Madrid ta wuce ta da maki 8 a saman teburin bayan ta lallasa Real Sociedad daci 2-0 a wasan da suka buga.
Labarai masu alaka
Read more at SOURCE: This post (Lionel Messi ya karya tarihin zakaran kasar Brazil, Pele bayan ya ciwa Barca kwallo guda a wasan data lallasa Valladolid 3-0) firstly published at hutudole.com on 2020-12-23 07:38:46
Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Thanks for visiting Arewasound.com