Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Mafiya yawan masu garkuwa da mutane mafi yawanci sun fito ne daga makwabtan jihar kano, wanne ya sa suke hadin gwiwa da jamian yankunan don inganta tsaron.
Rundunar ta ce hakan ne ya sa ta yanke shawarar cewa dole ne mutane su rika kula da kai komun mutane da ba su yadda da su ba a yankusan su tare da sanar da jami’an tsaro.
A hirarsa da manema labarai DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda shi ne kakakin rundunar yansanda ta jihar Kano ya ce lailai dole sai mutane sun kula sun kiyaye duk inda suka ji wani motsi ko hanzari da suka ga ba su yadda da shi ba su yi kokari su sanarwa da jami’an tsaro akwai kwamitoci da dama na yan Bijilanti da yan kwamiti, ba iya kano ba muna tsallakawa makwabtanmu da muke da boda da su irinsu Kaduna katsina duka muna hada karfi da su, don maganin wadanda suke tsallakowa suna aika aika.
Ya kara da cewa “jadawalin da muka fitar na garkuwa da mutane a wannan shekarar gaba daya, mun sami rahotanin garkuwa da mutane guda 18, idan ka hada da biyu na karya guda 20 kenan, ya ce mafi yawansu yan jihar kaduna ne sai katsina da jigawa su ne suke tsallakowa suke hada baki da namu na gidan suke aiwatar da wannan aika aika”.
Labarai masu alaka
Read more at SOURCE: This post (Mafi yawan masu garkuwa da mutane a jihar Kano ba ‘yan jihar bane>>PPRO) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 22:34:14
Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Thanks for visiting Arewasound.com