Connect with us
سبحان الله وبحمده سبحان الله العظيم

Labarai

Maganar Gaskiya, Sojojin Najeriya basu da isassun kayan yakin da zasu fuskanci Boko Haram>>Kashim Shettima

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Kashim Shettima ya ce babu isassun kayan da sojojin kasar ke bukata domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Sanata Shettima, wanda yanzu dan majalisar dattawa ne, ya yi gwamnan jihar Borno na shekaru 8, lokacin da ake tsaka da rikicin Boko Haram.

Ya yi kalaman ne a taron da kungiyar musulman Najeriya ta gudanar ranar Lahadi.

Kashim Shettima ya ce: “Kayan yakin da ake magana za a iya samunsu a Afirka ta Kudu ko Turkiyya ko Indiya ko Ukraine – za a same su a kasashe babu iyaka, kuma sojoji sun a da kuzari amma babu kayan aiki.

Boko Haram suna shan tramadol su kai wa sansanin sojoji hari. Abin da nake son fada shi ne muna bukatar a dauki matakan da suka dace, mataki na sojoji, da na tattalin arziki, da daukar mataki na kashin kamu,” in ji tsohon gwamnan.

A cewarsa, shugaban Najeriya ya gaza cimma wasu daga cikin muradunsa ne saboda ba ya bincike kan abubuwan da mutanen da ya nada a kan mukamai suke yi.

“Fisabilillahi nake fada, kawaicin shugaba kasa ya wuce gona da iri, sai ya nada mutum a mukami amma ba tare da tuntuba ba sai a bar mutum kara zube.

Shi mutumin da ne yana ganin kamar kowa kamar shi ne sannan kowa zai yi aiki. Ya kamata ya tabbatar da cewa duk kudin da aka ware domin sayen kayan aiki an saya amma wallahi tallahi maganar gaskiya babu kayan aiki,” a cewar Shettima.

Ya kara da cewa ya hadu sa sabon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya Janaral Attahiru, ya kuma nuna kuzari wajen aiki “kuma muna fatan nan ba da jimawa ba za a samu maslaha kan halin da ake ciki.”

Shettima ya ce ana bukatar sanin ta yadda za a farfado da tattalin arzikin arewacin Najeriya, saboda baki daya motocin tarakta 44,000 kadai ake da su a kasar, yana mai cewa “amma a jihar Uttar Pradesh da ke kasar Indiya suna da tarakta miliyan biyu da dubu dari uku.”

A cewarsa “duk irin hakilon da ake yi na inganta noma babu kayan aiki; akwai wani gwamna a arewacin Najeriya muna hira da shi na tambaye shi tarakta nawa yake da su ya ce ba su kai guda 20, kuma wai ita ce jihar da ake cewa ta na sahun gaba wajen samar da abinci.

Akwai wanda na tambaya injin cashe shinkafa nawa ake da su a jihar Kebbi? Aka ce min guda daya ne na gonar Sanata Adamu Aleiro, ban da shi babu wani inji a jihar. Dole ne mu rungumi fasahar zamani, kuma ba mai tsada ba ne, sannan muna da kwararrun yara da za su ilmantar da mutanenmu, saboda arewa ba mu da kasuwanci talauci ya mana katutu.”

Tsohon gwamnan na jihar Borno ya kara da cewa babban abin da ake bukata shi ne hadin kai domin kawo zaman lafiya.

“Rashin gaskiya, da rashin hadin kai da son zuciya, da duba abin da mutum zai samu na kashin kansa a kan me mutanenmu za su samu na zaman lafiya, shi ne babban matsalarmu. Muddin muka sanya cewa zaman lafiya shi ne a sahun gaba na abin da muke butaka to Insha Allah za a samu zaman lafiya. Sai kuma batun ilimi, samar da ilimi yana da matukar muhimmanci da inganta shi,” in ji Shettima.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[YARPP]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Maganar Gaskiya, Sojojin Najeriya basu da isassun kayan yakin da zasu fuskanci Boko Haram>>Kashim Shettima) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-19 16:39:09

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.