Connect with us
سبحان الله وبحمده سبحان الله العظيم

Labarai

Majalisar Dattawa ta nemi gwamnoni su aiwatar da cikakken ikon cin gashin kan bangaren shari’a

Published

on

Majalisar dattijai ta nemi gwamnonin jihohi 36 da su aiwatar da cikakken ikon cin gashin kai ga bangaren shari’a.

Opeyemi Bamidele, shugaban kwamitin majalisar dattijai a bangaren shari’a, ‘yancin dan adam da kuma lamuran shari’a, ya yi wannan bukatar lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Kungiyar ma’aikatan shari’a a Najeriya (JUSUN) a kwanan nan ta fara yajin aiki don nuna rashin amincewa da gazawar gwamnati na aiwatar da ikon cin gashin kai ga bangaren shari’a.

Bamidele ya ce ana bukatar bangaren shari’a mai zaman kansa don dimokradiyya ta gaskiya a Najeriya, ya kara da cewa babu wanda zai yi hasarar komai tare da irin wannan a bukutar.

“Babu wanda zai yi hasarar komai ta hanyar bayar da ‘yancin kai ga bangaren shari’a a matakin jiha tunda an yi hakan a matakin kasa,” in ji shi.

“Muna kira ga gwamnonin jihohi da su yi abin da ya kamata saboda ‘yancin cin gashin kai na bangaren shari’a ba abin tattaunawa bane.

“Babu dimokiradiyya da za ta iya rayuwa ba tare da an kafa ta a kan doka da kuma shari’a mai zaman kanta ba.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[YARPP]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Majalisar Dattawa ta nemi gwamnoni su aiwatar da cikakken ikon cin gashin kan bangaren shari’a) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-19 15:41:23

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.