Fa’izu Alfindiki, tsohon ma shawarci ga gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya lashe tikitin takarar shugabancin karamar hukumar birni karkashin jam’iyyar APC a zaben kananan hukumomin da za a yi a watan Janairun 2021.
Karamar hukumar birni na cikin guraran da ba’a iya cimma sulhu ba tsakanin ‘yan takarkarun tsakanain gidan Muntari Ishak tare da gidan Sha’aban Sharada wanda hakan ya tilasta shiga zaban fidda gwani, a karshe Al’findiki ya samu nasarar lashe tikitin kujerar zama Shugaban karamar hukumar.
A zaben fitar da gwanin da aka gudanar a ranar Asabar, Fa’izu Alfindiki ya samu kuri’u 423 inda ya kayar da Murtala Dandawaki wanda ya samu kuri’u 4 kacal.
Shugaban hukumar zaben, Yusuf Lafasa, ya ayyana Fa’izu Alfindiki a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu mafi yawan kuri’un da aka jefa yayin zaben.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan sanarwar, Faizu Alfindiki ya yaba wa Shugabannin Jam’iyya, jami’an zaɓe da takwarorinsa na sauran ƙananan hukumomin da suka yi masa fatan alheri.
Ya yaba wa mutanen da suka zabe shi, yana mai cewa kokarinsu ne ya kai shi ga nasara.
Labarai masu alaka