Garkuwa da Mutane Masu garkuwa da mutane sun sace Shugaban Karamar Hukumar...

Masu garkuwa da mutane sun sace Shugaban Karamar Hukumar Edo, tare da wasu fasinjojin motar bas

-

Masu garkuwa da mutane a jihar Edo, sun yi awon gaba da shugaban Karamar Hukuma, fasinjojin motar bas da kuma wani dalibin jami’a.

Shugaban da aka sace shi ne Waziri Edokpa, na karamar hukumar Esan ta tsakiya. An rahoto cewa anyi garkuwa dashi akan babbar hanyar Benin zuwa Abuja ran juma’a.

Edokpa, wanda farfesa ne a Sashin Lissafi  na Jami’ar Ambrose Alli, Ekpoma, an bayar da rahoton cewa an sace shi a safiyar ranar Juma’a.

Yayin da kurar da daga satar shugaban karamar hukumar har yanzu ba ta lafa ba, labari ya kuma zo cewa dukkan fasinjojin wani sanannen kamfanin jigilar kayayyaki da ke zaune a Benin ‘yan bindiga sun yi awon gaba da shi.

Direban motar bas din wanda aka ce yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Benin, an kashe shi.

Advert

Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba a san inda duk wadanda aka sace din suke ba.

An tattaro cewa shuwagabannin kananan hukumomin daga Edo ta kudu suna cikin wata ganawar sirri da kwamishinan yan sanda na jihar Edo, Johnson Babatunde Kokumo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you