Matar Jigon APC Bola Ahmed Tinubu za ta koma Majalisa

Hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta watau INEC, ta bayyana cewa Matar Asiwaju Bola Tinubu watau Sanata mai-ci Oluremi Tinubu ta sake lashe zaben da aka yi na ‘yan majalisa a makon da ya gabata.

Matar Jigon APC Bola Ahmed Tinubu za ta koma Majalisa

Sanata Oluremi Bola Tinubu ta jam’iyyar APC mai mulki ce ta yi nasara a zaben ‘dan majalisa mai wakiltar yankin Legas ta tsakiya. Oluremi Tinubu ta samu kuri’a 131, 735 ne inda ta doke ‘dan takarar PDP Onitiri David.

Hukumar INEC, ta bakin Malamin zaben ta watau Farfesa Oyeyemi Elijah Oyedola, ta bayyana cewa PDP ta samu kuri’u 89, 107 ne a zaben da aka yi. Hakan na nufin Misis Remi Tinubu za ta cigaba da rike kujerar ta bayan 2019.

KU KARANTA: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa yayi nasara a zaben 2019

Manyan jami’an INEC sun yabawa yadda aka yi zaben cikin lumuna ba tare da kawo wani tashin hankali ba. Remi Tinubu ta doke ‘yan takara fiye da 10 a zaben da aka yi. Za ta sake komawa majalisar tarrayya karo na 3.

Mai dakin tsohon gwamnan na Legas tana wakiltar kananan hukumomi 5 na cikin tsakiyar Legas wanda su ka hada da mazabar Lagos Island, Eti-Osa, Apapa, Surulere da kuma cikin Mainland a majalisar datttawan Najeriya.
Kun ji labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne yayi nasara a zaben shugaban kasa da aka yi a jihar inda ya doke ‘dan takarar jam’iyyar adawa, Atiku Abubakar, da kuri’u kusan 130, 000.

Leave a comment