Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Matashiyar da Mahaifinta ya aura mata Boka na neman Dauki

Published

on

Ku Taimaka Mani Babana Ya Aurar Da Ni Ga Boka-In Ji Latifah Yar Shekara 18

 

Wata yarinya mai suna Latifah ta kai kukanta gidan jaridar Zuma Times Hausa cewa mahaifinta ya aurar da ita ga wani dattijo boka dan shekara fiye 50 a Suleja.

Matashiyar da Mahaifinta ya aura mata Boka na neman Dauki

Matashiyar ta ce wannan mutumin watarana tana tallar masara ya zo ya tsaya a gabanta inda ya ce, ‘ba za ki ba ni masara ba ina matsayin babanki? Ni fa abokin babanki ne.”

 

Ta ce, ta dauki masara ta ba shi sai ya kawo dari biyar ya ba ta daganan ta ce ta rasa kansa bayan wani lokaci ya dawo ya ce zai kai kudin gaisuwa shekaru uku da suka gabanta inda ya amince.

 

“Bayan ya kai ne sannan washegari ya kai har da sadaki, daganan ne ta ji mutane na cewa boka wani kaza za ki auri boka ne fah! Daganan ne ta ce idonta ya kashe ta ce ba ta sonsa amma mahaifinta ya ce ba shi ba wannan maganar, aure sai an daura.

 

Daganan ne mahaifiyarta da ita suka shiga neman manya su shigo maganar wanda hakan ya kawo rabuwar mahaifiyar da baban yarinya har magana daga karshe magana ta kai kotun inda boka ya rubuta yarjejeniyar cewa ba ruwa shi da wannan yarinya kuma.

 

A cewar bayan ta saki jiki kawai sai ta ji mahaifinta ya daura mata aure da wannan boka inda ta ce jama’ar garinsu suna Allah Wadai da wannan aure.

 

“Na ce wa Babanta ita dai ba za ta taba zuwa gidan boka da sunan matarsa ba daga nan ne aka kulle ta a daki.
Ta ce da Allah Ya ba ta sa’a masu gadinta sun kau da jiki ne ta hau ta katanga ka gudo zuwa gare mu.

 

Latifah ta ce tuntuni ta yi tunanin shiga duniya amma ta zo ta yi tunanin bala’in da ke tattare da haka inda ta ke rokon a agaza mata a mahaifinta ya raba aurenta da boka Mahe don ya ce in ya ganta ko a kai sai an dauke zuwa wajen Mahe da ya daura mata aure da shi.

Menene shawarku ‘yan’uwa?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Matashiyar da Mahaifinta ya aura mata Boka na neman Dauki) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-08 05:20:54

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.