Labarai Messi yayi nasarar karya tarihin Macherano yayin da ya...

Messi yayi nasarar karya tarihin Macherano yayin da ya zamo dan wasan daya fi cin wasanni masu yawa da kasar Argentina

-

Tauraron dan wasan Barcelona, Lionel Messi yana cikin tawagar Argentina jiya yayin da suka yi nasarar lallasa kasar Peru 2-0 wanda hakan yasa yanzu kasar Argentina tayi nasara a gabadaya wasannin data buga na cancantar gasar kofin duniya.

Argentina tayi nasarar cin kwallayen ne ta hannun Gonzales da Lautaro Martinez yayin da shi kuma Messi yanzu yayi nasarar cin wasanni 85 da Argentina a wasanni 142 daya buga mata.

Wanda hakan yasa ya karya tarihin Javier Macherano wanda shi yayi nasarar cin wasanni 84 a wasanni 147 daya bugawa kasar. Messi ya kasance dan wasan daya fi ciwa Argentina kwallaye masu yawa a tarihi 71 kuma yanzu harin shi na gaba shine ya kara karya tarihin Macherano na bugawa kasar wasanni masu yawa.

Advertisements

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you