Mukoyi Lissafi Kashi Na Biyu 2

Mukoyi Lissafi 02

Karin Bayani
A posting din daya gabata munyi bayanin addition da subtraction wato hadawa da cirewa da wasu ka’idoji da dokokin da akebi idan za’a lissafasu. To yanzu kuma zamu cigaba akan wata ka’idar wacce ake sa brackets.

A darasin baya nabada wasu tambayoyi danace mai karatu idan yagane abun da mukayi bayani da ka’idojin to ya bada amsar wadannan tambayoyin.
(5) 60+-15=?
(6) -7+-3=?
(7) -4+39=?
(8) 3-5=?
(9) 5+6=?
.
To a ka’ida yanda na rubuta tambayoyin daga lamba ta shida(6) zuwa ta tara(9) akwai kuskure. Wannan kuskuren shine a ka’idar lissafi ba’a jera alaman hadawa(+) da cirewa(-) da ribanyawa(x) da rabawa(รท) ajere. Dole sai ansaka dayan acikin baka biyu wato brackets(). Kwata kwata bai kamata na rubutasu a haka ba, na rubuta su ahakanne saboda ayi saurin gane yanda ake lissafawa. Sai kuma agaba nayi bayanin cewa dole sai ansaka wasu a brackets.
(5) 60+-15=?
(6) -7+-3=?
(7) -4+39=?
.
Bai kamata na rubuta tambaya ta biyar a haka ba 60+-15=? A ka’ida lambar datake da negative sign ita za’asa acikin brackets. A doka da ka’idar lissafi haka yakamata nayi 60+(-15)=?
.
Amma asani inde lamba itace a farko to ba’a samata bracket koda kuwa negative lamba ce. Misali muduba tambaya ta shida(6) da ta bakwai(7):
-7+-3=?
-4+39=?
.
Idan mukace zamusa bracket a lambar datake da negative sign ta farko zasu zama haka kenan:
(-7)+(-3)=?
(-4)+39=?
.
To ba’ayin haka sai de ayisu kaman yanda mukayi akasa.
-7+(-3)=?
-4+39=?
.
Dafatan an fahinci wannan ka’idar.

DUBA WANNAN : Mukoyi Lissafi Kashi Na ‘Daya 1

Rubutawa : NURA MAHDI IDRIS

Leave a comment