Labarai NDLEA ta yi babban kamun tabar wiwi da ta...

NDLEA ta yi babban kamun tabar wiwi da ta kai naira miliyan 24

-

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wani dakin ajiyar wiwi a jihar Legas, inda ta kwace tabar wiwi sama da tan 5 da kudinsu ya kai kimanin naira miliyan 24.

 

Kwamandan NDLEA na Legas, Mista Ralph Igwenagu (kwamandan kwayoyi), yace a ranar Alhamis a baje kolin da akayi a Legas, an kwashe kayan tare da motocin alfarma 20 daga wurin ajiyar da ke yankin Ayobo na jihar Legas.

Advert

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa cafkewar tabar wiwi ita ce mafi girma da aka yi a cikin samame da akayi a cikin shekaru biyar da suka gabata a cikin jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you