kiwon lafiyaRAMADAN KAREEM : AMFANIN GANYEN ALAIYAHU.

RAMADAN KAREEM : AMFANIN GANYEN ALAIYAHU.

-

Alayyafu wanda ake kira (spinach a Turance) wata karamar ciyawa ce da ake shuka irinta a wurare da dama a kasashen Africa ciki harda Nigeria,inda abu ne mai wahala kaje a jihar da zaka rasa samun ganyen alayyafu a Nigeria.Wannan baya rasa nasaba da irin yanda mutane ke ta’ammali da shi dan muhimmancin nasa ga harkar da ta shafi kiwon lafiya ana sarrafa shi musamman ga abinci ko miya.
Alayyafu nada matukar amfani ga jikin mai cinsa domin kimiyya ta riga bankado wasu irin sinadirrai na musamman da jikin dan adam keda matukar bukata dasu a cikin alayyafu.Wadan nan sinadiran sun hada da :

 • Dietary fiber
 • Folate
 • Niacin
 • Panthothenic acid,
 • Pyridoxine,
 • Riboflavin,
 • Thiamine,
 • Vitamin C
 • Vitamin K
 • Vitamin E
 • Sodium
 • Potassium
 • Calcium
 • Copper
 • Iron
 • Magnesium
 • Manganese
 • Zinc
 • Lutein
 • Zeaxanthin
 • Cryptoxanthin
 • Carotene da makamantansu.

Alayyafu yana gyara lafiyar ciki (stomach health)

Yana sanyawa mutum yawan cin abinci da saurin narkarda abincin a cikin sauki(improves digestion)
Alayyafu kumshe yake da sinadirran Iron masu kara yawan jini a jiki.A dan haka mai fama da karamcin jini a jiki watakila kodan yawan jinya ko wani dalili na daban ko mai bukatar samun wadataccen jini a jiki musamman ga mace mai juna biyu to sai ya fake cin alayyafu da wake.
Amma a san adadin yawan da za a ci.


Alayyafu yana karawa garkuwar jikinmu karfi waton (immunity) wadanda sune ke yaqi da kwayoyin cutuka a cikin jininmu dan samarwa jiki da yancin kansa.Rauni ko karamcin garkuwar jiki yana iya zamowa musabbabin wasu rashin lafiyoyi ko yawan fama da ciwo akai akai.wannan baya rasa nasaba da irin dimbin sinadiran zinc da Vitamin C dake a cikinsa.A dan haka da ka sha kwayoyin Vitamin C a kullum gara ka ci alayyafu sau uku a sati.

Alayyafu na kara lafiyar ido ganin cewa kwashe yake da wasu sinadirrai kamarsu Lutein,Xanthene
,da beta carotene da aka yi amanna da cewa suna karawa idon mutum karfin gani da kuma haske.A dan haka mai gani bushi bushi ko yawan damuwar ido komai son ya kiyaye da yanayin lafiyar idonsa to ya zanka cin alayyafu a kalla sau uku a sati daya.

Alayyafu yana sanya karfi da kwarin kassan jiki (strong bones) saboda yana kumshe da sinadiran calcium da magnesium masu yawan gaske.

Alayyafu na kare mana cikinmu daga kamuwa da gyambon ciki(ulcers)
Alayyafu na taushe mana wasu rashin lafiyoyin da sauran abincin da muke ci basa iyawa.
Alayyafu na karfafa aikin kwakwalwa da daidaita yanda ya dace tayi aiki a tsakanin manya da kuma tsofaffi.

Cin ganyen alayyafu kan maida kwakwalwa fresh da kuma daidata tinani.
Ganyen alayyafu na daidata yawan kitsen da ya dace a jikin mutum.
Baya sanya kiba ko tara kitsen tumbi kamar yanda sauran abinci kayan maiko ke yi a jikin mutum.Asali yakan daidata kibar da ta dace ga jikin mutum.(maintain weight).
Alayyafu na ingata lafiyar zuciya da rage sinadiran cholesterol wadanda yawansu kan iya zamowa illa ga zuciya dan wasu cutukan zasu iya faruwa.

Alayyafu na kara yawan gashi wa jikin dan adam dan dauke yake da su vitamin B,C,and E.da su omega 3 fatty acid da potassium dukansu suna taka rawar gani dan samarda gashi wa jiki.
Alayyafu na kare jiki daga kwayoyin cuta na cutar daji waton cancer.

Alayyafu na samarwa jiki da natsuwa da kuma hutu.A sanda ka ci alayyafu to zaka ji ka samu gamsuwa da natsuwa dan akoi wasu sinadirrai kamar su magnesium da zinc daza su samar maka da bacci da kuma hutu.

Alayyafu na maganin anemia saboda kumshe yake da nin ba ninki na sinadiran Irons da ke samarda jini ga jiki.

Alayyafu na sasauta hauhawar jini a dalili da samuwar yawan sinadiran potassium a cikinsa.
Alayyafu na taimakawa wadanda suka kwana biyu wadanda yakasance ba kowane irin abinci ke gina masu jiki ba kuma ba kowane ya dace ace suna ci ba.

Sai dai kuma ba dan an ce alayyafu nada amfani ga jiki ba shi zai sa a fake cinsa a kullum safiya.Abinda ake bukata anan shi ne a zan ka bada tazara a sanda ake amfani da shi sai aci wani abinci na daban.kada a maida shi abinci na kullum kullum domin yawan cinsa kan kawo wani side effects.
Da fatar za a kula.
AMFANIN GANYEN ALAIYAFU.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you