LabaraiRuftawar gini yayi sanadin mutuwar mutane 8 tare da...

Ruftawar gini yayi sanadin mutuwar mutane 8 tare da jikkata mutane 20 a yayin shagalin bikin Aure a kasar Pakistan

-

Mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a lokacin da wani rufin gida ya rufta a wajen wani bikin aure, da aka gudanar a ranar Laraba a yankin Kurram Tribal da ke arewa maso yammacin kasar Pakistan, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa, a kalla mata 6 da yara biyu ne su ka rasa ransu a lokacin faruwar lamarin.

Hakanan rahotannin sun bayyana cewa, mutanan yankin da masu aikin ceto, sun ciro gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa dasu tare da wadanda suka jikkata, inda su aike dasu zuwa Asbiti mafi kusa domin kula da lafiyarsu.

Wani jami’in asibitin da aka kwantar da marasa lafiyan, ya shaidawa kafofin yada labarai cewa, mutane da dama sun ji munanan raunuka kuma suna kan basu kulawa.

Jami’in ya kara da cewa akasarin mutanen da suka jikkata mata ne da yara kanana.

(Xinhua / NAN)

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you