Singup Today 20points waiting For You.

Hello, Login to your account and access full feature Of AREWASOUND FORUM

Forgot Your Password? Request New One Now.

Lost your password? Please enter your email address. You will receive a link and will create a new password via email.

Captcha Click on image to update the captcha.

Sorry, you do not have a permission to ask a question, You must login to ask question.

Sakaci 1-5 Hausa novel

Sakaci 1-5 Hausa novel

Sakaci Hausa novel, Hausa novel sakaci , Hausa novels, sakaci

Tafiya ta ke yi mai cike da nutsuwa, cikin jerin likitoci da malaman lafiya, yadda ta ke tafiya a jerin y’an sahun gaba shine zai tabbatar maka da ita din ma babba ce, hakazalika duk inda ta gifta zaka ga mutane suna gaisheta manyansu da yaransu.

Matashiya ce wanda shekarunta ba za su gaza talatin da biyar (35) ba aduniya, ba fara ba ce sol haka kuma baza a kirata bak’a ba, ta na da idanu madai-daita had’e da dogon hanci wanda ya dai-daita da kyakykyawan fuskarta, karamin bakinta shi ya dad’a kawata kyawun fuskarta, tanada yalwataccen gashin gira da na ido ga kuma kwantattacen saje wanda shine zai nuna maka ta na da yawan gashi, baza kuma a kirata doguwa ba haka baza kuma a kirata gajera ba, sannan kuma ita ba siririya ba ce sai dai za’a iya saka ta a cikin jerin matan nan da aka fi sa ni da y’an duma-duma, komi dai na jikinta abin burgewa ne.

Sanye ta ke da atamfa samfurin holand mai kalan fari da kwalliyan blue, ta yane kanta da karamin gyale mai kalan blue, sannan takalmin da ke kafanta shi d’inma kalan blue ne mara tudu, sanye ta ke da farin gilashi mai kara karfin ido wanda ya amshi fuskarta.
Kai tsaye d’akin mata suka shiga wanda sukaci gaba da duba marasa lafiya cikin gwanan cewa da aikin.

Yadda ta ke mu’amala da marasa lafiya cikin wasa da dariya sukuma suna bata ansan duk abinda ta tambayesu ba tare da wata matsala ba abun ya dinga ba manyan likitoci fararen fatan da suke tare mamaki, kuma suka k’ara yaba kwazonta.

Ba wai sabon abu bane a wurin su, sai dai ganin cewan mafiya yawan likitoci a nahiyar africa basu fiye janyo marasa lafiyansu a jikinsu ba, hasalima sai kaga wasu sun d’au girman kai sun sawa kansu wannan yasa suka dinga ya ba mata.
Mamakinsu bai k’aru ba sai lokacin da suka kammala duba marasa lafiya, akan hanyarsu ta koma wa, inda mutane suketa gaisheta tamkar wata tauraruwa, wani daga cikin manyan likitocin ne wanda shi din ma farin fata ne ya kasa hakuri ya ce cikin harshen turanci
“Dr Farida tabbas kin cancanci a yaba miki, sai dai kuma fa ya kamata fa nima kibani wannan sirrin” ya k’arashe cikin sigar tsokana, sauran likitocin ma suka mata caa kowa da abinda yake fad’i ita kuwa badda murmushi ba abinda ta ke yi.

Isowarshi wurin shi yayi sanadiyar d’aukewa murmushin da ke kan fuskanta, kallo d’aya ta mai gami da sunkuyar da kanta, gabanta ne yaci gaba da fad’uwa had’e da shiga yanayin da ta saba tsintar kanta a duk lokacin da ta yi tozali da shi.
Hannu ya ba sauran likitocin suka gaggaisa ko kallon inda ta ke baiyi ba, bayan kammala gaishe-gaishe a tsakaninsu da kuma ta6a hira akan abin da ya shafi aikinsu ne d’aya da ga cikin likitocin ya ce cikin sigar wasa ” Dr Umar kai ma ya kamata ka rok’a mana Dr Farida ta ba mu wannan sirrin da ta ke anfani da shi wanda ya sa marasa lafiya suke kaunarta haka” ya fad’a cikin harcen nasara.

“Akwai wani mara lafiya da zan duba sai mun had’u a wurin review meeting” ya fad’a cikin basar da waccan maganar ba tare da ya basu ansa ba, bai jira me za su ce ba ya bar wurin cikin tafiyarsa ta kasaita.
Cikin wani irin yanayi tabar wurin baza ta iya cigaba da aikin ba saboda yadda ta ke jin zuciyarta, kai tsaye inda suka saba ajiye motocinsu ta nufa, don cigaba da zamanta a wurin zai iya haifar mata da bugawan zuciya.

Ta na shiga motarta ta fashe da wani irin kuka mai ta6a zuciyar duk wani mai sauraro, ita to mai zata yi wanda zai sa Dr Umar ya daina nuna mata wannan tsanar, sai da ta yi kuka kuka mai isarta kafin daga bisani ta yi ma motarta key ba dan kukan ya tsaya ba, haka tacigaba da kuka had’e da figar motar kai tsaye wani unguwa ta shige gamin da yin hon a kofar wani madai-daicin gida mai kyau, ba da jimawa ba wani dattijo yazo ya wangale kofar, wanda da alama shi ne maigadin wannan gidan, ba tare da ta ansa gaisuwar da ya mata ba, ta samawa motarta wurin parking.

  1. ≠≠≠≠≠≠≠Arewasound.com≠≠≠≠≠≠≠≠

Dattijuwar mace ce wacce a shekaru ba zata gaza shekaru arba’in da biyar (45) ba a duniya, ta na da d’an kiba sanna bak’a ce mai cikakken kamala.
Zaune ta ke akan kujera ta zaman mutum uku, labarai ta ke kallo a gidan talabijin din aljazira.

Yanayin yadda ta shigo falon shi ya janyo hankali wannan dattijuwar cikin tashin hankali ta kalle ta had’e da bud’e hannayenta duka biyu alamar tazo gareta, ba tare da 6ata lokaci ba Farida ta k’araso da gudu ta fad’a jikin dattijuwar, tunda dama ta na bukatar wanda zai rarrasheta.
Rungumota a jikinta ta yi ta kuma cigaba da shafa bayanta ba tare da ta yi magana ba haka nan kuma ba ta hanata kukan ba, idan da sabo ta saba da irin wannan yanayin da d’iyarta ta saba shugo mata a duk lokacin da suka had’u da Dr Umar dan haka yau d’in ma ba ta bukatar tambaya tasan shi d’in ne, sai da ta bari ta yi kukan sosai sannan ta goge mata hawaye had’e da ce wa.
“nasan ko baki fad’a min ba nasan Dr Umar ne ko” sake janyo ta jikinta ta yi ta cigaba da shafa bayanta alamar rarrashi, kafin daga bisani ta cigaba da cewa
“Anya Farida rayuwa zata yuwu a haka kuwa, bakya tunanin wani ciwo ya kama ki, ni na fad’a miki ki kwantar da hankalinki ki kuma bi shawarar da nake baki nasan zakiji dad’inshi amma kinki yarda ya kikeso na yi ne my dota?”

Sai a sannan Farida ta tsagaita da kukan, cikin dashewar murya ta ce ” Aunty bawai nak’i bin shawararki bane amma ni nasan cewa Dr Umar ya tsane ni ko kallona ba ya son yi, Aunty ki fad’a min ya zanyi, mai zanyiwa Dr ya daina nuna min tsana afili ya na hantarata, Aunty why mai yasa bazai gane k’addara ba?” Kukan ne ya dad’a kwace mata sosai.

Yatsa Aunty ta samata a baki alamar ta yi shuru, sannan ta kamo hannunta duka biyu ta had’a da nata sannan ta ce cikin tausayawa ” banaso ki dinga fad’an wannan kalamain dotana ni dai abin da na keso da ke shine ki kwantar da hankalinki sannan kisawa ranki Dr Umar bai tsaneki ba ya ma fi kowa sonki”
Cire hannunta ta yi daga na Aunty had’e da tashi ba tare da ta yi magana ba har sai da taje bakin kofar da zai sada ta da d’akinta kafin ta tsaya ba tare da ta juya ba ta ce
” Aunty karki manta babu abinda Dr Umar bai sani ba a game da ni, wannan dalilin ne yasa ya tsane ni na kuma tabbatar da ba zai ta6a sona ba, tabbas na cuci kaina”
Kuka ne ya kwace mata, ba tare da ta sake magana ba ta shige d’akin had’e da shigewa toilet dan d’auro alwala.

Ku jiramu don cigaba.

Arewasound.com , Hausa novels

Leave a comment

Danna {Allow}.👇 Don samun sabbin labarai akan lokaci. 💟Mungode💟
Dismiss
Allow