Ahmad Lawal Sanata Lawan ya musanta karbar cin hancin Naira biliyan...

Sanata Lawan ya musanta karbar cin hancin Naira biliyan biyu

-

Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Lawan, ya wanke hannunsa daga zargin karbar rashawa na Naira biliyan biyu don gaggauta sake nadin Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

 

Wannan martani na Lawan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Ola Awoniyi, ya fitar a yammacin jiya bayan da wata kafar yada labarai ta fitar da labarin wannan zargin cewa wata kungiya karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa ta karbi N2billion daga hannun Yakubu domin saukaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen nadin Professor Mahmood Yakubu a sabon wa’adin natsawon shekaru biyar.

Advertisements

Mista Ola Awoniyi ya kara dacewa wannan kafar yada labaran ta Kasa bada sunayen membobin kungiyar da kuma kwararan hujjoji, a don haka yana Kira ga alummar Nigeria da suyi watsi da wannan labarin na karya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you