Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Satar Daliban Zamfara: Ku sauka ko kuma kuyi maganin yan bindinga da yan ta’adda, – Hadimin Ganduje ya fadawa Shugaba Buhari da sauran Gwamnoni

Published

on

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Satar Daliban Zamfara: Ku sauka ko kuma kuyi maganin yan bindinga da yan ta’adda, – Hadimin Ganduje ya fadawa Shugaba Buhari da sauran Gwamnoni

Mashawarci na musamman ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni kan su yi murabus ko kuma magance matsalar yan bindinga da yan ta’addan da ke addabar kasar.

Ya ce jam’iyyar APC mai mulki, a dukkan matakai sun gaza musamman wajen kare rayukan da dukiyoyin masu jefa kuri’a wadanda suka kawo su kan mulki.

Yakasai ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Juma’a dangane da sace daliban mata 317 da aka yi a daren Alhamis a Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.

Wasu daga cikin sakon na cewa: “A bayyane yake, mu a matsayin mu na gwamnatin APC, a kowane mataki, mun gazawa kare rayuka da dukiyoyi yan Nageriya da suka zabe mu.

Babu ranar da zata wuce ba tare da an samu matsalar rashin tsaro a wannan kasar ba.

Wannan abun kunya ne, ku gaggauta magance matsalolin ko kuyi murabus.

Satar Daliban Zamfara: Ku sauka ko kuma kuyi maganin yan bindinga da yan ta’adda, – Hadimin Ganduje ya fadawa Shugaba Buhari da sauran Gwamnoni

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

CHECK OUT
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

Read more at SOURCE: This post (Satar Daliban Zamfara: Ku sauka ko kuma kuyi maganin yan bindinga da yan ta’adda, – Hadimin Ganduje ya fadawa Shugaba Buhari da sauran Gwamnoni) firstly published at hutudole.com on 2021-02-27 03:45:44

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.