Shirin Wasan Kwaikwayon Gidan Badamasi Arewa24

Gidan Badamasi Arewa24

Gidan Badamasi sabon film din wasan barkwanci ne da ake dauki-ba-dadi a tsakanin wasu irin ‘ya’ya masu kunnen kashi da mahaifinsu Alhaji Badamasi.

Alhaji Badamasi dattijon attajiri mai kimanin shekaru saba’in yayi aure da dama a rayuwarsa, inda ya haife ‘ya’ya masu yawan gaske, wasu ma bai San Ina suke ba a halin da ake ciki.

A wannan wasan kwaikwayo an fara samu sabani ne daga lokacin da Alhaji Badamasi ya kasa cika alkawarin kudi da ya yiwa ‘ya’yansa.

Yaki ya barke tsakanin marowacin uba da handamammun ‘ya’ya. Ba’a taba kirkirar film kamar gidan badamasi a kasar hausa ba. Fim ne na barkwanci mai dauke da nishadantarwa da ilmantarwa ta hanyar amfani da gwanayen ‘yan wasan barkwanci ta yadda mutum zai yi ta zura idanu yana jiran ganin abin da zai faru a nan gaba.

SOURCE AREWA24

Leave a comment

Related Posts

Izzar So - Episode 18 - Session 2 - The