Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta lyon, Moussa Dembele yana shan gwagwarmaya sosai a wannan kakar yayin da wasanni biyu kacal ya fara bugawa kungiyar tashi daga farko tun da aka fara buga gasar Ligue 1 a watan oktoba.
Sannan dan wasan kwallo guda kacal yaci a wannan kakar a wasan su da Reims na watan nuwamba, bayan ya ciwa Lyon kwallaye 24 a kakar bara wanda suka hada da kwallaye biyu daya ci a wasan da suka lallasa Manchester City 3-1 a gasar zakarun nahiyar turai.
Sakamakon rashin kokarin da dan wasan yake yi a wannan kakar yasa yanzu manema labarai suna bayyana cewa kungiyar Lyon zata siyar da dan wasan nata a watan janairu.
Manajan Lyon, Rudi Garcia ne ya bayyana cewa dan wasan nashi ya samu rauni kuma bai fadi lokacin da dan wasan zai warke ba, yayin da ya kara da cewa yana so kungiyar shi tayi nasara akan Nantes domin sun basu kashi a kakar bara.
Kungiyar Lyon ta kasance ta biyu a saman teburin gasar Ligue 1 yayin da taui nasarar cin wasanni 13 a jere bayan ta lallasa Nice daci 4-1 a ranar sati.
Labarai masu alaka
Read more at SOURCE: This post (Tauraron dan wasan kungiyar Lyon, Moussa Dembele ya samu rauni a hannun shi yayin da suke gudanar da atisayi) firstly published at hutudole.com on 2020-12-23 12:24:39
Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Thanks for visiting Arewasound.com