Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, a ranar Lahadi ya ce ba shi da niyyar sauya sheka zuwa jam’iyyar (APC) ko kuma wata jam’iyyar siyasa.
Da yake magana da manema labarai a jihar Katsina bayan kaddamar da Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP, Shema ya karyata jita-jitar da ake yadawa kan wasu hotuna da aka gansu tare da Gwamna na yanzu, Alhaji Aminu Bello Masari, a yayin bikin nadin Kanal AbdulAziz Musa Yar’Adua (mai ritaya) a matsayin Mutawallen Katsina, wanda ya gudana a fadar mai martaba Sarkin Katsina.
Hoton ya jawo ce-ce-ku-ce kan cewa tsohon gwamnan na shirin sauya sheka zuwa APC.
Shema ya bayyana cewa hoton na ‘yan uwantaka ne kawai, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da kasancewa a PDP kuma zai yi aiki don ci gaban jam’iyyar a babban zabe mai zuwa.
Labarai masu alaka