Labarai Wani tsohon malamin KADPOLY ya harbe matarsa tare da...

Wani tsohon malamin KADPOLY ya harbe matarsa tare da kansa.

-


– Ana zargin wani tsohon malamin KADPOLY da kashe kansa

– Sai da Austin Umera ya harbi matarsa, sannan ya kashe kansa

– Har yanzu ba a gano dalilin da zai sa babban mutum irinsa ya kashe kansa ba

Wani tsohon malamin KADPOLY, mai suna Austin Umera ya shayar da mutane mamaki a kan abinda ya aikata.

Ana zarginsa da laifin harbin matarsa, Dokta Maurin, wacce ita ma malama ce a jami’ar jihar Kaduna (KASU), inda daga bisani ya harbe kansa kuam ya fadi ya mutu.

Al’amarin ya faru ne a gidansu da ke layin Kigo a cikin garin Kaduna.

Yanzu haka Dokta Maurin tana kwance a asibitin sojoji na 44 da ke cikin Kaduna, inda ake cigaba da kulawa da lafiyarta.

An adana gawar mijinta a ma’adanar gawa dake asibitin kwararru na Barau Dikko a Tudun wada.

Jaridar Daily Trust ta samu labarin wannan mummuna al’amarin ne da misalin karfe 10 na daren Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you