Wata mata ta mutu a gidan kula da tsofaffi ‘yan sa’o’i kadan bayan an mata allurar rigakafin Covid-19 a Queensland, Australia.
Yan sanda na Queensland sun tabbatar da cewa matar mai shekaru 82 ta mutu ne a ranar Laraba, 7 ga Afrilu, kuma ba a dauki mutuwarta kamar wani abin zargi ba.
Matar na zaune ne a gidan kula da tsofaffi na Yurana a cikin Springwood a kudu maso gabashin Queensland kuma ta karbi allurar rigakafin da misalin karfe 10 na safiyar yau, in ji Courier-Mail.
Babu tabbas ko mutuwar matar tana da nasaba da allurar rigakafin saboda tana fama da rashin lafiya da dama, gami da cutar huhu.
Wani mai magana da yawun ‘yan sanda ya fadawa Yahoo News Australia cewa za a shirya rahoto game da binciken lamarin.