Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Kungiyar Chelsea tayi nasarar komawa ta biyar a saman teburin gasar Premier League, bayan ta lallasa West Ham 3-0 ta hannun Silva da kuma Tammy Abraham wanda yaci mata kwallaye biyu a wasa guda karo na farko tun a satumba a shekarar data gabata, yayin da yaci kwallaye uku tsakanin su da Wolves.
Tauraron dan wasan Chelsea Timo Werner yanzu ya buga wasanni 7 kenan a jere ba tare ya zirawa kungiyar shi kwallo karo na farko tun shekara ta 2016, yayin da shi kuma Mason Mount ya zamo dan wasan ingila mafi karancin shekaru daya bugawa Chelsea wasanni 50 na gasar Premier League, yana dan shekara 21 tun bayan John Terry a a shekara ta 2002.
Wasa daya kacal Chelsea ta fadi cikin wasanninta na gida guda 13 da suka gabata, yayin da take karawa da zakarun gasar wato Liverpool a watan satumba na shekarar data gabata.
Labarai masu alaka
Read more at SOURCE: This post (West Ham 0-3 Chelsea: A karo na farko Timo Werner ya buga wasanni bakwai a jere ba tare da ciwa kungiyar shi kwallo ba tun shekara ta 2016) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 07:37:22
Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot
Thanks for visiting Arewasound.com