Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Ya umarce ni da in cire kayan jikina amma na ki”>>wata yarinya ta ba da labarin yadda wani mutum ya yanke hannunta da adda saboda kin amincewa da fyade

Published

on

Ya umarce ni da in cire kayan jikina amma na ki”>>wata yarinya ta ba da labarin yadda wani mutum ya yanke hannunta da adda saboda kin amincewa da fyade

Wata yarinya ‘yar shekaru 16 da haihuwa, babbar daliba a Gundumar Bududa, Uganda, ta ba da labarin yadda wani mutum ya tare mata hanya inda ya yanke mata hannu bayan ta bijire wa yunkurin yi mata fyade.

Evelyn Namasopo ta fada wa Babban Magistrate na Mbale, Mista James Mawanda, yayin wani zama a Kotun Majistare ta Bubulo da ke Gundumar Manafwa a ranar Laraba, 7 ga Afrilu, cewa wanda ake zargin Derrick Kuloba, mai shekara 25, ya kai mata hari a kusa da wani daji a kan hanyarta ta zuwa gida don karbowa mahaifiyar dake kwance a asibiti abinci.

Evelyn ta ce ta yi kuwa da ihu da fatan samun taimako amma a banza, ta kara da cewa har yanzu tana fama da radadi mai yawa.

Ya umarce ni da in cire kayan jikina amma na ki”>>wata yarinya ta ba da labarin yadda wani mutum ya yanke hannunta da adda saboda kin amincewa da fyade

Wacce abun ya shafa tayi zargin yan sanda da Kotun Mbale da kokarin murkushe kararta saboda an sake Kuloba a wani yanayi da ba a san shi ba‘ yan kwanaki kadan bayan kama shi.

Mai gabatar da kara ya shaidawa kotu cewa Kuloba, mazaunin Kauyen Nabooti, ​​Nakatsi Sub-County a cikin Gundumar Bududa, a ranar 4 ga Yulin, 2020 dauke da adduna, ya tare mata hanya kuma ya far mata da niyyar yi mata fyade, bayan taki amincewa sai ya sare mata hannu.

Ya umarce ni da in cire kayan jikina amma na ki”>>wata yarinya ta ba da labarin yadda wani mutum ya yanke hannunta da adda saboda kin amincewa da fyade

Yarinyar kuma ta samu raunuka da dama a wasu sassan jiki. Mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu uku; wanda abun ya shafa, dan uwanta da kawunta.

A cikin shaidar ta, yarinyar ta kara rokon kotu da ta yiwa Kuloba hukunci mai tsauri.

An daga karar zuwa 8 ga Afrilu, 2021 lokacin da ake sa ran Mai gabatar da kara zai gabatar da karin shaidu a kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Ya umarce ni da in cire kayan jikina amma na ki”>>wata yarinya ta ba da labarin yadda wani mutum ya yanke hannunta da adda saboda kin amincewa da fyade) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-08 11:32:53

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.