Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

kiwon lafiya Yan Bautar Kasa 11 Sun Kamu da Cutar COVID-19...

Yan Bautar Kasa 11 Sun Kamu da Cutar COVID-19 a Sansanin Yan Bautar Kasa na Jihar Taraba

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Akalla mambobi masu bautar kasa (NYSC) goma sha daya ne suka kamu da cutar Coronavirus a sansanin yan bautar kasa na Jihar Taraba.

Kwamishinan lafiya na jihar Taraba, Innocent Vakkai ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Jalingo, babban birnin jihar.

Yan Bautar Kasa 11 Sun Kamu da Cutar COVID-19 a Sansanin Yan Bautar Kasa na Jihar Taraba

Vakkai ya ce, ‘yan yi wa kasa hidiman da suka kamu an tabbatar da cewa ba su nuna wata alama kuma suna amsar magani a wani kebabben wuri a jihar.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa an yi wa membobin bautar kasar gwajin ne bisa umarnin da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayar cewa duk mambobin shirin za a gwada su a lokacin da suka iso sansanonin daban-daban.

An gano yan bautar kasa 11 tare da cutar a jihar Taraba lokacin da suka isa sansanin.

”Don haka a matsayin wani bangare na jagororin kwamitin da ke fadar shugaban kasa a kan COVID-19 kan kula da COVID-19 a Najeriya, sun nemi kowace jiha da ta gudanar da gwaji mai yawa ga dukkan mambobin bautar da ke sansanoni kuma a jihar Taraba an gwada mambobi goma sha daya da ke dauke da cutar amma dukansu basu nuna alama, ma’ana, ba sa nuna alamun cutar.

”Tunda suna da cutar, abin da ya rataya a wuyan hukumomin lafiya don tabbatar da cewa an kebe su.

.

“Dangane da bayanan da na samu ya zuwa yanzu, duk suna cikin koshin lafiya kuma nan ba da jimawa ba za su sake haduwa da danginsu yayin da sansanin ke rufewa,” inji shi.

Vakkai, wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin a kan COVID-19 a jihar ya nuna bakin ciki tare da rashin bin matakan tsaro da mazauna jihar ke dauka don rage yaduwar cutar tsakanin al’umma.

Ya dage cewa akwai hatsarin mai jira a gaba idan ba a rage sakaci ba.

Ya yi kira ga mazauna da su kasance masu kamewa da yin taka tsan-tsan, musamman a wannan lokacin na bukukuwan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Read more at SOURCE: This post (Yan Bautar Kasa 11 Sun Kamu da Cutar COVID-19 a Sansanin Yan Bautar Kasa na Jihar Taraba) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 13:48:48

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you