Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Jigawa Yan bindiga sun kashe jami'in dan sanda bayan sun...

Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda bayan sun sace’ yar tsohon shugaban karamar hukuma da wasu mutane biyu a Jigawa

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani dan sanda yayin da suke kokarin ceto wasu mutane biyu da aka sace a kauyen Bosuwa da ke karamar hukumar Maigatari a jihar Jigawa.

Kakakin rundunar, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar DAILY POST a Dutse.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 2:00 na safe a kauyen Bosuwa.

Jinjiri ya ce masu garkuwar wadanda yawansu ya kai tara, sun afka wa kauyen ne a kan babura dauke da muggan makamai inda suka yi awon gaba da mutane biyu.

Wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da Alhaji Ali Dankoli mai shekaru 70 da Zainab Isah mai shekaru 25, wacce diya ce ga tsohon shugaban karamar hukumar, Maigatari, Isa Zakari Bosuwa.

“‘ Yan sanda a Maigatari sun samu kiran waya cewa wasu ‘yan daba wadanda yawansu ya kai tara da muggan makamai sun afkawa wani kauye da ake kira Bosuwa suka tafi da mutum biyu daga dangi daban-daban.

“Yan sanda sun garzaya wurin, sun toshe duk hanyar shigowa da wuraren wanzuwan kauyen sannan suka bai wa‘ yan bindigar wuta.

“Yayin da suke kokarin tserewa sai suka bude wuta a kan ‘yan sandan da ke kokarin ceton wadanda aka sace,” in ji shi.

Ya ce sakamakon haka, jami’in dan sanda daya ya mutu kuma masu aikata laifin suka gudu.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan ‘yan sanda a jihar Jigawa sun ceto wani mai suna Ibrahim Bronco wanda wasu‘ yan bindiga suka sace a karamar hukumar Jahun da ke jihar bayan sun yi masa fashin kudi N140,000.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Read more at SOURCE: This post (Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda bayan sun sace’ yar tsohon shugaban karamar hukuma da wasu mutane biyu a Jigawa) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 10:20:59

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Karanta Wannan:-  Cristiano Ronaldo ya zamo dan wasa mafi yawan kwallaye a tarihin tamola

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you

Karanta Wannan:-  An cafke jami'in tsaron jami'ar ABU Zaria da ake hada baki dashi ana sace mutane