Labarai Yan Bindiga sun shiga wani yanki a Abuja sun...

Yan Bindiga sun shiga wani yanki a Abuja sun sace ‘yan gida daya su 5

-

Yan Bindiga a yankin Pegi dake Kuje, Abuja sun shiga wani gida inda suka sace mutane 5 ‘yan gida daya.

 

Wadanda aka dace din sune Jubril Abdullateef (22), Sherifat Abdullateef (20), Muyidat Abdullateef (13), Nura Abdullateef (18) da Nahimat Abdullateef (9). An sace su a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba.

 

Wani dake zaune a yankin ya bayyanawa Dailytrust cewa mahaifin wanda aka sace din baya gida inda yana dayan gidan matarsa yayin da lamarin ya faru.

 

Advert

Yace kamin zuwan ‘yansanda tuni an wuce da wanda aka sace din. Hakanan shima kakakin hukumar yankin ta Pegi, Oyedeji Oyetunji ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kakakin ‘yansandan Abuja, ASP Mariam Yusuf tace suna shirin fitar da sanarwa ta musamman akan lamarin kuma suna kokarin ceto wanda aka sace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you