Labarai 'Yan matan da ake zargi da yinkurin kashe gwamnan...

‘Yan matan da ake zargi da yinkurin kashe gwamnan Osun sun bushe da dariya bayan da aka karanto sumu karar, abinda ya baiwa alkali haushi

-

Advertisements
Advertisements

Wasu ‘yan mata 2, da ake zargi da yunkurin kashe gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola sun baiwa mai shari’a Olusegun Ayilara haushi bayan da suka bushe da dariya bayan jin abinda ake zarginsu dashi.

 

Wannan yasa alkalin ya bada umarnin a tsaresu. ‘Yan matan sune, Suliyat Tajudeen da Ayomide Abdulaziz wanda shekarunsu basu wuce 20 ba.

 

Ana zargin ‘yan matan da lalata motoci 17 ne da satar waya da Kwamfutar tafi da gidanka da kuma yunkurin kashe gwamna.

 

Saidai a daidai inda aka zo cewa ana zarginsu da yunkurin kashe gwamna sai ‘yan matan suka kasa rike dariyar da suke suka bushe da dariya. Hakan yasa alkain ya jawo hankalinsu da cewa zargin da ake musu ba na wasa bane.

Advert

 

Saidai dukansu sun musanta zargin da ake musu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you