Crime 'Yan Sanda A jihar Neja sun cafke wasu Mutane...

‘Yan Sanda A jihar Neja sun cafke wasu Mutane 3 da ake zargi da laifin satar man fetur

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da dibar man fetur daga bututun da aka lalata a kauyen Numba-Gwari da ke karamar hukumar Suleja ta jihar.

Bututun wanda mallakar kamfanin man fetur na kasa ne (NNPC).

Jami’in hulda da jama’a na rundunar (PPRO), ASP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a  wata sanarwa da ya fitar a Minna.

Abiodun ya bayyana hakan da cewa, a ranar 13 ga watan Nuwamba da misalin karfe 09:00, rundunar ‘yan sandan jihar ta yi nasarar cafke wadanda ake zargin biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu.

Haka zalika rundunar ta bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka Daniel Joshua, Mai shekaru 37, sai  Sunday Ezekiel, Mai shekara 33 da Suleiman Madaki, Mai shekaru 29, dukkaninsu mazauna kauyen Numba-Gwari da ke Suleja.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you