Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Labarai Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Fashi...

Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Fashi da Makami 5 a Abuja

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Rundunar ‘yan sanda ta babbab birnin tarayya ta cafke wasu da ake zargin‘ yan fashi da makami ne a Wuse Zone 1, Abuja.

Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Bala Ciroma, wanda ya bayyana hakan yayin gabatar da wadanda ake zargin a shalkwatar rundunar da ke Abuja, a jiya, ya ce jami’an’ yan sanda daga reshen Wuse ne suka cafke su yayin da suke sacewa mutane kayayyakinsu masu muhimmanci.

Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Fashi da Makami 5 a Abuja

Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifinsu yayin da ake yi musu tambayoyi cewa suna da alhakin aikata laifi a kan hanyar Wuse.

Ya bayar da sunayen wadanda ake zargin kamar su Sanusi Ibrahim, Salim Umar, Kabiru Umar, Shamsudeen Rabiu da Ibrahim Shehu.

A cewarsa, daga cikin kayayyakin da aka kwato daga wadanda ake zargin sun hada da agogon hannu guda 8 na zinariya, iPads guda biyar, kwamfutar tafi-da-gidanka guda biyar, katin ID 25 da katin ATM, kayan adon zinare da azurfa guda 33.

Ya kara da cewa an samu nasarar kwato Dirham din UAE 30, kudi CFA dubu 3, 100 Rand na Afirka ta Kudu, N25,000, adduna uku da takobi guda a hannun su, yana mai cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

Kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su hanzarta kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba a yankin na su.

“Yayin da rundunar ke son tabbatar wa mazauna kudurin ta na dakile aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaro a cikin babban birnin tarayya yayin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, ana shawartar jama’a da su kuma kira lambobin wayar nan idan akwai wani gaggawa ko damuwa – 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883, ”in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Read more at SOURCE: This post (Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Fashi da Makami 5 a Abuja) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 10:29:19

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you