Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Adamawa Yan sanda sun fasa wata kungiyar masu garkuwa da...

Yan sanda sun fasa wata kungiyar masu garkuwa da mutane a Adamawa, sun ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Adamawa ta fasa wata kungiyar masu satar mutane tare da kubutar da wasu mutane biyu a cikin maboyar kungiyar.

Jami’an rundunar da suka afka wa maboyar sun yi nasarar kame mambobin kungiyar tara wadanda yanzu haka suke hannun ‘yan sanda.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Suleiman Nguroje ya fitar, ya bayyana cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin‘ yan asalin garin Dapshi ne da ke jihar Yobe sun shigo Adamawa ne, sun dauki sauran 7 din kuma sun kafa kungiyar satar.

Nguroje ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda wadanda aka zakulo daga sashin’ yan sanda na Song, sun yi nasarar kubutar da wani Babawuro Damuwa da kuma wani Yarima Musa na garin Song a yayin samamen da suka yi a maboyar masu garkuwar.

Ya bayar da sunayen wadanda ake zargin kamar haka Ndam Usai (29), Buba Adam (22), Buba Alim (39), Bodi Kulawal (25), Sale Musa (28), Babiri Gula (23), Abayel Ahmadu (28) , Sani Muhd ​​(24) da Abdullah Hassan (36).

Ya bayyana cewa ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne bayan da suka hada baki, suka sace tare da neman kudin fansa miliyan 4 daga iyalan Babawuro da Yerima.

“Bayan samun rahoton, kwamishinan‘ yan sanda Olugbenga Adeyanju, ya tura jami’an tsaro na ‘yan sanda da mafarauta wadanda daga karshe suka ceto wadanda lamarin ya rutsa da su kuma suka cafke wadanda ake zargin.

“Bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa wadanda ake zargi na farko da na biyu sun fito ne daga jihar Yobe inda suka dauki mutum na uku zuwa na tara da ake zargi kuma daga karshe sun kirkiro wata kungiyar da za ta gudanar da ayyukan satar mutane,” Nguroje ya bayyana.

Read more at SOURCE: This post (Yan sanda sun fasa wata kungiyar masu garkuwa da mutane a Adamawa, sun ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 09:10:20

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Karanta Wannan:-  Hukumar sojin Najeriya ta fara daukar aiki, Duba yanda zaku nema

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you

Karanta Wannan:-  Chelsea 3-1 Luton:Tammy Abraham ya zamo dan kasar Ingila na farko daya ciwa Chelsea kwallaye uku a wasa guda tun Frank Lampard a shekara ta 2007