Smart News EverydayAREWASOUND
سُبحَانَ اللّهِ وَ بِحَمْدِهِ ، سُبحَانَ اللّهِ الْعَظِيمِ

Labarai Yan sanda sun gurfanar da mutum 5 bisa zargin...

Yan sanda sun gurfanar da mutum 5 bisa zargin satar wayar abokin zaman su ta N76,000

-

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Yan sanda a ranar Litinin sun gurfanar da mutane biyar da ake zargi a gaban Kotun Yankin Karu na 1, Abuja kan zargin satar wayar abokin kwanan su da ta kai N76,000.

 

Wadanda ake tuhumar suna fuskantar shari’a kan tuhume tuhume biyu na ayyukan hadin gwiwa da kuma sata wanda suka musanta aikata laifin.

Yan sanda sun gurfanar da mutum 5 bisa zargin satar wayar abokin zaman su ta N76,000

Wadanda ake tuhumar su ne: John Felix, 18, Williams James, 18, Oche Bernard, 22, Idris Mohammed, 17 da Osama Saleh, 19.

 

Mai gabatar da kara, Ayotunde Adeyanju ya fadawa kotun cewa mai shigar da karar, Emmanuel Michael na Kasuwar Karu, Abuja ya kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Karu a ranar 9 ga Nuwamba.

 

Adeyanju ya fadawa kotun cewa mai shigar da karar ya yi zargin cewa a wannan ranar, yayin da yake barci a adireshin da muka ambata a sama, wadanda ake tuhumar sun hada baki a tsakanin su kuma cikin rashin gaskiya sun saci wayarsa kirar Infinix da kudin ta ya kai N76,000.

 

Ya ce laifin ya ci karo da sashi na 79 da 288 na Penal Code.

 

Alkalin kotun, Inuwa Maiwada ya bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi N20, 000 kowannensu tare da wanda zai tsaya musu guda daya sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu, 2021, don ci gaba da sauraren karar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Read more at SOURCE: This post (Yan sanda sun gurfanar da mutum 5 bisa zargin satar wayar abokin zaman su ta N76,000) firstly published at hutudole.com on 2020-12-22 14:01:25

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Karanta Wannan:-  Katsina spends over N3bn on running gov’t monthly – Official  – Katsina Post

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

You might also likeRELATED
Recommended to you

Karanta Wannan:-  Caccakar da Jega yawa Gwamnatin Buhari ta tabbatar da abinda muke fada akan shi>>PDP