Connect with us
Ramadan KAREEM

Labarai

Yan sandan Jihar Adamawa sun kame magidanci da ake zargi da kashe wani tsoho mai shekaru 57 da yake zargin yana tare da matarsa

Published

on

Yan sandan Jihar Adamawa sun kame magidanci da ake zargi da kashe wani tsoho mai shekaru 57 da yake zargin yana tare da matarsa

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Adamawa a ranar Laraba 7 ga Afrilu, ta gabatar da wani saurayi dan shekara 27, Johnson Samuel, wanda ya daba wa wani tsoho dan shekaru 57 wuka har lahira saboda zargin cewa yana saduwa da matarsa.

Rahotannin sun bayyana cewa wanda ake zargi da kisan, mazaunin ƙauyen Bandasarga ne, dake cikin karamar hukumar Ganye ya dawo gida a ranar Lahadi, 4 ga Afrilu, 2021 tsakanin ƙarfe 11 zuwa 12 na dare kuma ya haɗu da tsohon a gidansa.

Ya yi zargin cewa tsohon ya yi lalata da matarsa, kuma a cikin fushi ya daba masa wuka.

Wanda aka dabawa wuka mai suna Yaji Lawal, mazaunin kauyen Bakari guso, an garzaya da shi asibiti amma likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


CHECK OUT
[related_posts_by_tax]
How to Setup Glo Unlimited Browsing 2021

Airtel Bonus Code You Can’t Miss 2021

SOURCE: This post (Yan sandan Jihar Adamawa sun kame magidanci da ake zargi da kashe wani tsoho mai shekaru 57 da yake zargin yana tare da matarsa) firstly published at www.hutudole.com on 2021-04-07 21:46:54

Start Arewasound Bot for more News anytime.t.me/arewasound_bot

Thanks for visiting Arewasound.com

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Copyright © 2012 Present | Powered by AREWASOUND LTD.