Mafi yawan lokuta mutane kan yiwa Gawayi kallan abun banza kai wasu kan Dauki Gawaki a matsayin bama shi da wani Amafani.
Wasu kuwa Sun Dauki Amfanin Gawayi shine girka abinci ko ko Jin Dumi a lokutan sanyi, a tunanin su wannan shine iya Amfanin sa.
Sai dai abun ma iya cewa sam ba haka bane, hakika gawayi yana da matukar amfani kama ga amfani da muke dashi na yau da kullum kai harma ga lafiyar jikin mu.

Kadan Daga cikin wasu Al’fanun da Gawayi kedashi.
MAGANIN KURAJE DA GYARA FUSKA
Da farko za’a daka gawayi akwaba da zuma a shafa afuska, bayan minti 30 awanke.
MAGANIN KORE WARI
idan daki ko wani lungu a cikin gida na wari ko cikin takalmi, asa gawayi
aciki zaidaina.
MAGANIN HANA RUBEWA
idan ba aso ‘ya’yan itace su rube da wuri, sai asa su acukin gawayi su kwana, haka kuma idan ba ason kunu yayi
tsami sai asa gawayi aciki ya kwana.
MAGANIN GYAMBO
adaka gawayi arika sawa,
zai busar da gyambon ya kame.
MAGANIN INGANTA RUWA
a saka gawayi a cikin ruwa mai datti, yana taimakawa wajen kwantar da dattin cikin ruwa.
Yana sake gyaran miyar da ta dauki lalacewa Idan miya ta dauki lalacewa in ta kwana da safiya kawai kar ka zubar nemi gawayi ka jefa cikin miyar a dora kan wuta a dumama zai dawo da darajar miyar kamar da.