Labarai Yanda wasu hatsabibai suka kona dansandan Najeriya suka kuma...

Yanda wasu hatsabibai suka kona dansandan Najeriya suka kuma ci namansa

-

Jami’an ‘yansanda a jihar Oyo sun kama wasu da ake zargi su 2 da hannu a kisa da kuma kona gawar dansandan Najeriya suka kuma ci namansa a yayin zanga-zangar SARS.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da kamen a sanarwar da ya fitar, yau, Asabar.

 

Wanda aka kama din wata matace me ciki yar kimanin shekaru 34 da wani dan shekaru 43 kjma tuni aka mayar da binciken da ake kansu zuwa babban ofishin ‘yansandan dake Abuja.

 

Advertisements

A jawabin matar, tace ba gaskiya bane zargin da aka mata na cin naman dansandan. Tace tabbas ta halarci wajan da lamarin ya faru amma dayan namijin da aka kamasu tarene ya bata ajiyar naman dansandan.

 

Shima dai dayan da ake zarginsu tare yace tabbas yana wajan da lamarin ya faru amma dai maganar gaskiya ita matarce da kanta ta dauki wani sashen jikin dansandan inda ta nemi ya bata abinda zata saka ciki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

You might also likeRELATED
Recommended to you