Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya sanar da nadin mukaddashin shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta jihar Neja, Alhaji Ahmad Garba Gunna (Dan Majen Kagara), a matsayin sabon Sarkin Kagara.
Nadin sabon Sarkin ya biyo bayan rasuwar tsohon Sarki, Alhaji Salihu Tanko Kagara, a ranar 1 ga Maris, 2021 bayan fama da rashin lafiya a Minna, babban birnin jihar.
Gwamnan, ta bakin Kwamishinan Kananan Hukumomi, Ci gaban Al’umma da Harkokin Masarauta, Malam Abdulmalik Sarkin Daji, ya bayyana hakan a Minna a ranar Laraba bayan karbar rahotannin masarautun 14, karkashin jagorancin Alhaji Ibrahim Muhammad (Madakin Gunna).
Gwamna Bello ya ce nadin sabon Sarkin ya kasance daidai da sashi na 3 karamin sashe (1) na dokar Sarakuna (Nadawa da Nadin Sarauta), Fasali na 19, dokar jihar Neja.