Kungiyar Real Madrid ta ziyatci Inter Milan ranar 25 ga watan nuwamba ba tare da tauraron dan wasanta ba wato Sergio Ramos amma duk da haka tayi nasarar lallasa su 2-0 a wasan da suka buga.
Raphael Varane da Nacho ne suka tsare baya a wasan kuma sun jajirce sosai yayin da gabadayan su suka yi nasarar dakatar da hare haren da Inter Milan ta kai ta hannun Romelo Lukaku da kuma Lautaro Martinez.
Kocin Madrid Zidane ya bayyana cewa Varene dan wasan Madrid ne kuma shi din bana siyarwa bane gami da harin shi da kungiyar Manchester United take yi bayan da suka tashi wasan nasu.
Shima Varane ta tofa albakacin bakin nashi bayan an tashi wasan inda yake cewa Madrid zata buga wannan kakar cikin nasara kuma sunyi kokari sosai a wasan da suka buga da Inter Milan.
Labarai masu alaka